Bidiyon Tsiraici: Daurawa ya goge bidiyon kamen Hafsat Baby

0

Wasu majiyoyi a Hukumar Hisbah ta Jihar Kano sun tabbatar wa Aminiya cewa Hafsan Baby tana tsare a hannun hukumar.

Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya goge bidiyon da ya wallafa na kamen jarumar TikTok, Hafsat Baby, wadda hukumar ta kama kan yin bidiyon tsiraici.

A safiyar Litinin ce Sheikh Daurawa ya wallafa bidiyon Hafsat Baby tare da wasu mata da hukumar ta kama.

Wasu majiyoyi a Hukumar Hisbah ta Jihar Kano sun tabbatar wa Aminiya cewa Hafsan Baby tana tsare a hannun hukumar.

Sai dai sun ƙi su bayyana lokacin da hukumar ta cika hannu da jarumar TikTok ɗin.

Aminiya ta lura cewa bayan kimanin sa’o’i biyu, Sheikh Daurawa wanda a halin yanzu yake ƙasar Jamus, ya goge sakon bidyon kamen Hafsat.

Ana iya tuna cewa a kwanakin baya hukumar ta sanar cewa an yi kutse a shafinta, lamarin da ya sa a halin yanzu ba za iya dogaro da wani daga shafin ba.

Aminiya ta yi ƙoƙarin zantawa da jami’an Hisbah kan kamen Hafsat Baby, amma hakan bai samu ba.

Jami’an da muka tuntuɓa sun bayyana cewa kasancewar Litinin ɗin ranar hutun Takutaha ce da Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana, ranar Talata idan aka dawo aiki za a ji halin da ake ciki game da Hafsat Baby.

Aminiya ta ruwaito cewa ɓullar bidiyon tsiraicin matashiyar a kafofin sada zumunta ta haifar da ce-ce-ku-ce, inda daga bisani Hisbah ta kama ta.

Hafsat Baby dai ta yi ƙaurin suna da yaɗa abubuwa marasa kyau waɗanda ke yawan jawo ce-ce-ku-ce a Soshiyal Midiya.

A kwanakin baya, bayan Hisbah ta kama ta tare da yi mata nasiha, matsayar ta sanar cewa ta tuba, kuma ta goge duk miyagun abubuwan da ke shafinta na Tiktok.

Daga bisani ne bidiyon tsiraicin nata ya fito, inda ake ganin hakan a matsayin alamar tuban muzuru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *