Tsohon ɗanwasan Real Madrid da Man Utd, Varane ya yi ritaya daga taka leda
Tsohon ɗanwasan Manchester United da Faransa Raphael Varane ya yi ritaya daga taka leda yana ɗan shekara 31.
Varane ya koma tamaula a ƙungiyar Como ne a watan Yuli a kyauta, amma ya ji rauni a wasansa na farko da suka fafata da Sampdoria a watan Agusta.
Sai dai ɗan wasan bayan, ya ce zai cigaba da kasancewa a ƙungiyar a wani matsayin daban ba na taka leda ba.
“Ba ƙaramin ƙarfin hali mutum yake buƙata ba wajen ɗaukar irin wannan matakin na sauroron jikinsa da zuciyarsa. Ina so ne in yi ritaya da mutuncina ba wai in cigaba da tilasta jikina domin buga ƙwallo ba,” kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Instagram.
Varane ya fara taka leda ne a ƙungiyar Lens ta Faransa, inda ya yi kaka ɗaya kafin ya koma Real Madrid a shekarar 2011.
Ya yi shekara 10 a ƙungiyar ta Spain, inda ya lashe kofi 18, ciki har da La Liga 3 da Champions Leagues huɗu.
Daga nan ne ɗan wasan ya koma Manchester United a farkon kakar 2021 a kan farashin farko na Fan miliyan 34, inda ya taka wasa guda 95 a dukkan gasanni duk da fama da raunuka da ya yi.
Ya lashe kofin Carabao a Manchester United a shekarar 2022, sannan wasansa na ƙarshe a ƙungiyar shi ne wasan ƙarshe na kofin ƙalubale wato FA, inda United ta doke Manchester City a watan Mayu.
A ƙasarsa ta Faransa, ya buga wasa 93, inda ya lashe Gasar Cin Kofin Duniya a shekarar 2018 da Gasar Nations League a 2021, sannan yana cikin tawagar Faransa da suka sake kai wa wasan ƙarshe a Gasar Cin Kofin Duniya a shekarar 2022.
“Na sha faɗuwa sannan in tashi, amma a wannan lokacin, yana ganin ya kamata in haƙura da tamaula,” in ji shi.
“Ba na da-na-sanin komai saboda babu abun da zan iya canjawa. Na samu nasarorin da ban taɓa zato zan samu ba. Sannan bayan nasarar lashe kofuna, ina alfaharin cewa duk runtsi duk wahala na kasance mutum mai gaskiya, sannan kuma duk inda na je, sai da na bar baya mai kyau. Ina fata na saka ku farin ciki da alfahari.”
A game da abin da zai fuskanta, Varane ya ce, “Zan cigaba da gudanar da harkokin ƙwallon ƙafa amma ba a matsayin mai bugawa ba. Zan bayyana a nan gaba kadan.”
Varane ɗan wasan baya ne mai kyau, wanda wasu suke ganin rauni ya hana rawar hantsi, har ya kai ga ya yi ritaya.